Atiku Abubakar yayi Allah wadai da kashe kakakin jam’iyyar PDP da aka yi
- Atiku yayi Allah wadai da kashe mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP na jihar Adamawa
- Atiku Abubakar ya mika ta'aziyar sa ga iyalan Sam Zadoch
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, yayi Allah wadai rikicin da ake yi a jihar Adamawa, wanda yayi sanadiyar mutuwar mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP na jihar Adamawa, Sam Zadock, da mutane 12.
A jawabin da Atiku Abubakar, ya fitar a ranar Laraba, yayi Allah wadai da rikicin addini da ya barke tsakanin Musulmai da Kristoci Kudancin jihar Kaduna a ranar Litinin wanda yayi sanadiyar asara rayuka da dukiyoyi a jihar.
Abubakar, ya nuna damuwar sa akan yadda kashe-kashe da tashin hankali ya zama ruwan dare a Najeriya.
KU KARANTA : Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP
A ranar Laraba jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar, Mista Sam Zadoch ta sanadiyar rikici da ya barke tsakanin ‘yan tawayen kabilar Bachama da makiyaya a yankin Numan Demse a ranar Talata.
Atiku Abubakar ya mika ta’aziyar sag a iyalana Zadok da mutanen da rikicin ya shafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng