Kimiyya da fasaha: Wasu yan sama jannati guda 3 sun dawo daga aikin watanni 5 a Duniyar Wata

Kimiyya da fasaha: Wasu yan sama jannati guda 3 sun dawo daga aikin watanni 5 a Duniyar Wata

Rayuwa kenan, kowa da kiwon da ya karbe shi, a yayin da wasu al’umma basu da burin da ta wuce samun abincin da zasu ci sau uku a rana, wasu kuwa bukatarsu shi ne su shiga Duniyar wata don binciken kwakwaf.

Da safiyar ranar Laraba 28 ga watan Feburairu ne wasu masana kimiyya da fasaha suka dawo Duniyarmu daga Duniyar wata, inda suka kwashe watannin biyar da rabi a can suna binciken kwakwaf tare da gudanar da wasu ayyuka na musamman.

KU KARANTA: Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta

Mutanen su uku, guda biyu yan kasar Amurka, Joe Acaba da Mark Vande Hei, 1 kuma dan kasar Rasha, Alexander sun dira ne a wani yanki dake tsakanin kasar Rasha da kasar Kazahstan, kamar yadda Voa-muryar Amurka ta ruwaito.

Kimiyya da fasaha: Wasu yan sama jannati guda 3 sun dawo daga aikin watanni 5 a Duniyar Wata
Mutanen

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutanen sun gudanar da aikin gayaran wani mutum mutumi ne da aka tura duniyar wata don aikace aikacen da suka shafi kimiyya da fasaha tare da gudanar da binciken kwakwaf a can.

Sai dai da fari hukumar kimiyya da fasaha ta Amurka,NASA, ta yi hasashen cewa ba lallai mutanen su iya sauka ba, saboda tsananin sanyi da karfin iska, wanda da hakan ya faru da shikenan sai dai su yi ta bulayi a sararin samaniya, amma duk da haka sai ga shi sun sauka, amma fa da kyar.

Kimiyya da fasaha: Wasu yan sama jannati guda 3 sun dawo daga aikin watanni 5 a Duniyar Wata
Mutanen

Majiyar ta ruwaito saukansu ke da wuya, sai jami’an kula da lafiya suka rufesu da wasu manyan barguna, sa’annan suka tafi dasu son basu kulawan da ya dace. A yanzu haka akwai sauran wasu guda uku dake can Duniyar watan basu dawo ba, suna gudanar da aikace aikace daban daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng