Babban hafsan sojojin sama ya koma Maiduguri don jagorantar farautar 'yan makarantan Dapchi (hotuna)
- Babban hafsan sojojin sama ya koma Maiduguri
- Hakan na cikin kokari da ake na ganin an ceto yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram suka sace
- Rundunar ta girke jiragen yaki domin farautar yan matan
Rahotanni sun kawo cewa shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadik Abubakar, ya koma Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Shugaban sojin zai jagoranci ceto yan matan makarantar sakandare na garin Dapchi day an ta’addan Boko Haram suka sace.
Ya sha alwashin cewar dakarunsa za su yi aiki tukuru ba dare ba rana domin ganin sun kubutar da yara 'yan makarantar daga hannun kungiyar Boko Haram.
Kawo yanzu, rundunar sojan saman Najeriya ta girke manyan jiragen saman yaki tare da kayayyakin aiki domin ceto yaran.
KU KARANTA KUMA: Yusuf Buhari ya sadu da mahaifinsa bayan dawowa daga hutun jinya (hoto)
Jiragen yakin wanda suke tashi daga birnin Maiduguri suna shawagi a sararin samaniyar hanyoyi da dajukan da suka hada birnin Maiduguri da jihar Yobe.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng