Harbin bindiga domin murnar biki ya aika ango barzahu

Harbin bindiga domin murnar biki ya aika ango barzahu

- Wani harsashin bindigar da aka harba yayin wani biki ya yi ajalin wani ango a kasar Indiya

- Wani daga cikin 'yan biki ne ya harba bindiga ana tsaka da casu amma sai harsashin ya fada kan angon

- An garzaya da angon asibiti amma kafin likitoci su dora hannu a kan shi tuni rai ya yi halin sa

Wani harsashi da ya fita daga wata bindiga da aka harba yayin shagalin biki a New Delhi ya zama ajalin wani ango

An harbe angon, Deepak Kumar, mai shekaru 21 a yayin da ake cikin tsaka da bikin raka shi dakin amaryar sa a ranar Talata.

Harbin bindiga domin murnar biki ya aika ango barzahu
Harbin bindiga domin murnar biki ya aika ango barzahu

'Yan sanda sun sanar da cewar wani daga cikin 'yan bikin ya harba bindigar yayin da yake rawa tare da ragowar jama'a amma sai harsashin ya fada kan ango kuma ya zama ajalin sa.

DUBA WANNAN: Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

"An garzaya da shi asibiti amma da misalin karfe 12 na dare sai aka sanar da mu ya mutu," a cewar Nupur Prasad, mataimakin kwamishinan 'yan sanda a New Delhi, kamar AFP ta rawaito.

Harbin iska a yankin Asiya yayin shagalin biki ba bakon abu ba ne.

Kasar Indiya ta haramata hakan amma har yanzu jama'a ba su daina ba.

Prasad ya ce iyalin angon sun ce sun san wanda ya yi harbin tare da bayyana cewar hukumar 'yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng