Rikici a Baburar Jigawa: An kashe mutane biyu an kona motoci biyar

Rikici a Baburar Jigawa: An kashe mutane biyu an kona motoci biyar

- Garin babura yana kan iyakar Najeriya ne da Nijar

- Kwasta m sun kashe wani dattijo ne da direbansa

- Daruruwan mutane sun far ma ofishin da hari

Rikici a Baburar Jigawa: An kashe mutane biyu an kona motoci biyar
Rikici a Baburar Jigawa: An kashe mutane biyu an kona motoci biyar

A jihar Jigawar arewacin Najeriya, an sami wasu gungun samari da suka farma ofishi da jami'an kwastam da ke girke a yankin cikin fusata inda suka barnata dukiyoyi da tada rikici da ya haddasa mutuwar mutum har biyu.

An kuma kone motocin hukumar da ma ofisoshinta na yankin mai makwabtaka da Nijar, inda masu fasa-kwabri kan bi su shigo da ababen da aka hana shigo dasu kamar shinkafa da motoci.

Rikicin dai a cewar masu gani da ido, ya faru ne sakamakon harbe wani dattijo dan shekara 60 da ma direbansa a makon nan, da ma'aikatan hukumar suka yi, kuma suka mutu.

DUBA WANNAN: Hukumar Kwastam sunyi manyan kamu

A yanzu dai rahotanni na cewa komai ya lafa, bayan mutuwar dattijo Alhaji Ummaru babban mutum, wanda yaje ofishin hukumar domin ceto motarsa da hukumar suka kama, da alama ta fasa-kwabri ce.

Ance ma'aikacin kwastam ya harbe shi a ciki, direbansa kuma a kafa, inda ba da dadewa ba ya cika har lahira, abun da ya tunzura samarin kenan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng