Aiki sai mai shi: Jami’an DSS sun bindige wasu gagararrun yan bindiga a jihar Zamfara

Aiki sai mai shi: Jami’an DSS sun bindige wasu gagararrun yan bindiga a jihar Zamfara

Hukumar tsaron sirri, DSS, ta sanar da sunayen wasu gaggan masu garkuwa da mutane, cikin wadanda take nema ruwa a jallo a sassan kasar nan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Daga cikin wadanda hukumar ta bayyana sunayensu akwai Barnabas Torva Amadi mai inkya Ataminin, daya daga cikin wadanda suka kashe dan wani dan majalisan jihar Taraba, Hosea Ibi. Sauran sun hada da Aondi TERSOO, Nengenen Mbaawuaga DAMIAN, Aondoase KAYITOR da Ternenge TERSOO.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar ta cafke Abubakar Muhammed (Gamere) Usman UMARU aka Dan Gurgu; Abubakar UMARU, Garba UMAR aka Smally, Abubakar GARBA; da Umar BELLO, barayin dake addaban hanyar Lkoja zuwa Okene, wadanda suka saci yan Amurka a jihar Kaduna.

Bugu da kari a sun kama Anthony Kio Elegwe, shahararren barawon mutane, wanda ya sace Marie Ebibake, tshohuwar kwamishinan sufuri na jihar Bayelsa, tare da cafke Umar ABUBAKAR (aka Small), Abubakar AHMADU (aka Sarkin Yaki), Aliyu ABUBAKAR (aka Koroko), Aliyu MOHAMMED (aka Chogo) and Abubakar UMARU (aka Bokolori) dake addaban hanyar Kogi zuwa Edo.

Kaakakin DSS, Wilson Uwajere ya tabbatar baya da kakkama yan bindigan, sun karkashe wasu da dama bayan musayawar wuta a garuruwa da dama a dukkanin fadin Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel