Da dumi-dumi: Kifi ya hadiye N52 Million a jihar Abia
Rahoton da muke samu na bayyana cewa wani kifi ya hadiye kudi N52 million na cibiyar cigaban kasuwanci na yankin kudu maso gabas da kuma gina cibiyar karfafa mata a jihar Abiya.
Jaridar The Nation ta tattaro rahoton cewa an baiwa kamfanin Phrenemos Intl Ltd kwangilan ne kuma sakataren gwamnatin jihar Abia, Dakta Eme Okoro ne ya kamata ya lura da yadda ake aikin.
Kafin yanzu, an kasance ana zargin sakataren gwamnatin jihar da almundahana da babakere da kudaden kwangololi da kuma amsan cin hanci daga hannun yan kwangila.
Bincike ya nuna cewa sakataren gwamnatin tarayyan da aka baiwa aikin lura ya fadawa kamfanin Phrenemos Intl Ltd cewa su bude asusun banki a UBA tare da wata Glory Emucha da sunan cewa da bankin gwamnatin Abia ke aiki, ashe aljihunsa yakewa aiki.
Bayan makonni, shugaban kamfanin Phrenemos Intl Ltd , Engr Emma Uche Adimoha ya garzaya bankin UBA domin sanin halin da ake ciki amma aka fada masa wani kifi ya hadiye kudin.
Ya tabbatar da cewa sun kara sanya wani kudi N2million cikin asusun amma wannan kifinya sake hadiyewa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng