Babban magana: Ana shirin maka Ganduje a kotu
- Mazauna garin Janguza, karamar hukumar Tofa dake jihar Kano na shirin maka gwamnatin jihar a kotu
- Hakan ya biyo bayan saba ma wata yarjejeniya da gwamnatin Kano tayi akan diyar fili
- Gwamnatin Kano ta amince da komawar gidan kurkuku na Kumawa zuwa kauyen Janguza
Sama da mutane 70 dake zaune a Janguza, wani garin manoma a karamar hukumar Tofa dake jihar Kano, ke kokarin maka gwamnatin jihar Kano a kotu sakamakon saba ma wata yarjejeniya akan diyar fili.
Mazauna garin sun yi zargin cewa gwamnatin tarayya tare da ta jihar Kano sun hada hannu wajen kwace gonakin da suka gada daga magabatansu domin gina kurkuku ba tare da an biya su diya ba.
Idan za a tuna gwamnatin jihar Kano ta amince da komawar gidan kurkuku na Kumawa zuwa kauyen Janguza.
Rahotanni sun kawo cewa tuni gwamnatin tarayya ta tura masu gini wajen sannan kuma an fara aiki.
Sai dai mazauna yankin sun nuna damuwarsu kan matsayar hukumomi game da biyan diya ga wadanda abun ya shafi gonakinsu.
KU KARANTA KUMA: Sace yan mata: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi
Mazaunan sun yi korafin cewa duk da cewan gwamnatin tarayya da ta jiha sun yi alkawarin biyan diya ga masu gonaki a baya, babu abunda aka ba mafi akasarinsu.
Sunyi korafin cewa mutane shida kawai aka biya inda kimanin mutane 70 ke jiran tsammani.
A wani al'amari na daban bisa kokarin ganin an magance karancin kananan kudade a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, babban bankin Najeriya ya fara wani shiri bisa kudirin ganin an cika kasuwanni da kananan kudade.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng