Jami'in kwastam ya harbe wani a Jigawa

Jami'in kwastam ya harbe wani a Jigawa

- 'Yansanda sun kama wani jami'in hukumar kwastam da ya kashe wani mutum a garin Babura dake jihar Jigawa

- Hukumar yansadar jihar Jigawa ta ce ta kwantar da tarzomar da ya so a ya barke a Babura sakamakon harbe wani mutum da jami'in kwastam yayi

'Yansandar jihar Jigawa, ta kama wani jami’in hukumar fasakwabri da ake zargin sa da harbe wani mutum a karamar hukumar Babura dake jihar Jigawa.

Wani dattijo da abun ya faru a gaban sA, ya fadawa manema labaru cewa al'amarin ya faru ne lokacin da wani mutumin mai suna, Alhaji Ummaru, yayi kokarin shiga tsakanin jami’an hukumar kwastam a lokacin da suka biyo wani direba da ya shigo cikin garin Babura.

"Wannan abu yasa wani jami'in kwastam ya harbe shi, " Inji mutumin.

Ya ce a take a wurin 'yan uwan mutumin suka suka garzaya da shi asibiti bayan a harbe shi kafin ya mutu.

Jami'in kwastam ya harbe wani a Jigawa
Jami'in kwastam ya harbe wani a Jigawa

Wannan al’amari ya janyo fusatattun matasa sun kona rumfunan kasuwanci da ke kusa da ofishin kwastam dake Babura.

KU KARANTA : Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandar jihar Jigawa, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari inda ya ce suna tsare jami'in hukumar kwastam din da ya yi harbin.

Ya kuma ce tuni aka aike da jami'an tsaro domin kwantar da tanzomar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng