Maza ku auri mata fiye da daya inda hali - Inji wata likita
Kamar yadda kishi ya zamo kumallon mata ta yadda babu mace dake son wata ta rabi mijinta da sunan kishiya, wata likita da aka ambata da suna Hauwa Ibrahim wacce ta kasance ma’abociya ce ta kafar sada zumunta tab a maza shawara kan su airi mata sama da guda daya idan har suna da halin yin haka.
Hauwa ta bayar da wannan shawara ne a kokarinta na ganin an kawar da aikata fasikanci da maza masu aure ke aikatawa na bin matayen banza a waje.
"Ya ku Maza bayan zama Miji na gari, ku kokarta wajen kara auren Mace ta biyu idan kuna da ikon yin hakan. Ga wadanda suke da biyu su kara ta uku, masu uku su kara ta hudu. Wannan babbar Sunnah ce ya kuma fi Alheri fiye da yin lalata da mata a waje" kamar yadda tawallafa a shafinta.
A nata ganin bin wannana shawara zai rage yaduwar fasikanci tsakanin ma'aurata.
KU KARANTA KUMA: Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN
Jama'a da dama sun tofa albarkacin bakin su kan batun. Mafi yawanci maza sun yaba mata bisa shawarar data bayar. Sai dai akwai wadanda suka yi hannun riga da wannan shawarar tata.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata mata mai suna Fatima Mohammad mai shekaru akalla 16 a duniya ta shaidawa wata kotun da ke zama a Abuja yadda tsananin kyaunta ke hana ta zaman lafiya da mijinta mai suna Tasi'u Kasim da suka shafe shekaru biyu tare.
Matar, Fatima Mohammad dai ta doshi kotun ne sannan kuma ta roke ta da ta taimake ta ta raba auren nasu don kuwa a cewar ta tuni zaman lafiya yayi kaura a tare da ita da mijinta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng