Shugaba Buhari ya baiwa jahohin Najeriya bashin Naira 1.9 tiriliyan daga asusun rarar man fetur
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta ayyana cewa har ya zuwa watan Satumbar shekarar da ta gabata ta 2017, ta rabawa jahohin Najeriya 36 bashin akalla Naira 1.91 tiriliyan daga asusun rarar mai watau Excess Crude Account (ECA) a turance.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo shine ya bayyana hakan a jiya, garin Abuja lokacin da ya jagorancin wani zaman tattaunawa da nufi lalubo hanyoyin magance matsalar cin hanci da rashwa.
KU KARANTA: NNPC zai gina matatar mai a Arewa
Legit.ng ta samu cewa mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa duba da yadda gwamnatin ta bayar da wadannan kudaden, ba bu gwamnatin baya tun daga shekarar 1999 zuwa 2015 da ta yi hakan.
Haka ma dai Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma'aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.
Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin bayanin maraba da babban ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Sanata Chris Ngige ya yi jiya Litinin lokacin da yake jawabi a lokacin bikin cikar kungiyar kwadago ta kasa shekara arba'in da kafuwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng