Barkonon tsohuwa ya kashe wani dalibi yayin artabun 'yan daba da 'yan sandan Najeriya

Barkonon tsohuwa ya kashe wani dalibi yayin artabun 'yan daba da 'yan sandan Najeriya

An samu kazamin tashin hankalin a unguwannin Akala da kuma Idi-Oro dukkan su dake a karamar hukumar Mushin ta jihar Legas a jiya Talata tsakanin wasu gungun 'yan daba da kuma 'yan sandan Najeriya dake yankin inda kuma hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyar ciki hadda dalibin makaranta.

Majiyar mu dai ta ruwaito cewa rikicin ya soma faruwa ne a dai dai lokacin da tawagar 'yan sanda suka kai samame a wata maboyar 'yan shaye shaye a unguwannin wanda hakan yayi sanadiyyar gwabza fada.

Barkonon tsohuwa ya kashe wani dalibi yayin artabun 'yan daba da 'yan sandan Najeriya
Barkonon tsohuwa ya kashe wani dalibi yayin artabun 'yan daba da 'yan sandan Najeriya

KU KARANTA: NNPC ta amince ta gina matatar mai a Arewa

Legit.ng ta samu cewa sai dai a kokarin su na ganin sun kama masu shaye-shayen, yan sandan sun kuma jefa barkonon tsohuwa a cikin wasu makarantun sakandare na kudi dake a kusa da inda masu shaye-shayen suke wanda hakan ne ma ya janyo mutuwar dalibin.

Haka ma dai, Labari mai dadin da muke samu daga majiyar mu na nuni ne da cewa sojoji da kuma mafarauta sun samu nasarar kashe wasu manyan mayakan kungiyar nan ta Boko Haram dake ci gaba da yaki da jami'an tsaro a garin Madagali, jihar Adamawa.

Haka nan ma mun kuma samu cewa mayakan na Boko Haram sun samu nasarar kashe wasu mazauna garin na Madagali su 3 a yayin harin da suka kai masu a jiyan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng