Yadda ta kwashe a tsakanin yaron wani tsohon gwamna da EFCC a gaban kuliya manta sabo

Yadda ta kwashe a tsakanin yaron wani tsohon gwamna da EFCC a gaban kuliya manta sabo

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta tasa keyar yaron tsohon gwamnan jihar Filato, Nanle Miracle Daniel gaban Kotu kan badakalar kudi N1.5bn.

Sahara Reporters ta ruwaito a zaman kotun na ranar Talata 27 ga watan Feburairu, EFCC ta tuhumi Nanle da aikata laifuka guda shidda da suka danganci sata da kuma karkatar da kudade a gaban Alkalin babbar Kotun tarayya Abuja, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

A shekarar 2013 ne dai Nanle ya boye ma hukuma wani cinikkaya da aka yi a Otal dinsa mai suna La Paris La Paradise, da ta kai ta naira biliyan 1.5 ta asusun bankin Otal din, wanda hakan yaci karo da dokar da ta kayyade kudin da kowanni Otal za ta iya amsa, Naira miliyan 10.

Yadda ta kwashe a tsakanin yaron wani tsohon gwamna da EFCC a gaban kuliya manta sabo
Nanle

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nanle ya musanta dukkanin zarge zargen da EFCC ke yi masa, wanda hakan ya sanya Alkalin Kotun dage shari’ar don sanya ranar fara sauraron karar, zuwa 10-12 na watan Afrilu, kamar yadda lauyan mai kara ya bukata.

Hakazalika Kotun ta bada belin wanda ake kara, kamar yadda lauyansa ya bukata, inda ta umarce shi ya biya Naira miliyan 5, tare da kawo mutane biyu manyan jami’an gwamnati da zasu tsaya masa, tare da biyan miliyan 5 kowannensu.

Yadda ta kwashe a tsakanin yaron wani tsohon gwamna da EFCC a gaban kuliya manta sabo
Nanle

Abinka da masu hannu da shuni, tuni Nanle ya gabatar da Amana Yusuf, ma’aikaciyar gwamnati a mataki na 12 dale aiki da ma’aikatar tsaro, da kuma Uwargida Rose ma’aikaciya a mataki na 13 dake aiki a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng