Sabon salo: Yadda iyaye mata a Ghana ke yiwa yara bilicin tun su na ciki

Sabon salo: Yadda iyaye mata a Ghana ke yiwa yara bilicin tun su na ciki

- Mata ma su juna biyu a kasar Ghana na shan wasu kwayoyi domin yiwa 'ya'yan su bilicin tun su na ciki

- Kwararru a bangaren kiwon lafiya sun gargadi matan a kan illolin dake tattare da yin hakan

- Wannan sabuwar al'ada na kara samun karbuwa a tsakanin Mata ma su juna biyu a kasar ta Ghana

Wani sabon salon son samun farar fata ya bullo a kasar Ghana, inda mata ke shan wasu kwayoyi da za su yiwa jariran su dake ciki bilicin.

Sai dai kwararru a bangaren kiwon lafiya sun yi gargadi cewar akwai illa matuka dangane da yin hakan.

Bincike ya tabbatar da cewar Mata masu juna biyu kan sha kwayar glutathione domin yin mayar da fatar jariran su dake ciki ta koma fara.

Sabon salo: Yadda iyaye mata a Ghana ke yiwa yara bilicin tun su na ciki
Yadda iyaye mata a Ghana ke yiwa yara bilicin tun su na ciki

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci (FDA) ta ce ba ta amince da amfani da maganin domin yin bilicin ga jariran dake ciki ba domin ba don haka aka yi maganin ba.

Duk da gargadin masanan, mata masu juna biyu na cigaba da shan kwayar domin bilicin ga jariran su. Sai dai hukumomin tsaro sun fara cafke mutane da kamfanonin dake shigo da kwayar maganin.

DUBA WANNAN: Ma'aurata sun sha bulala a bainar jama'a saboda yin aure babu yardar iyayen su

Ana shigo da kwayar maganin ne ta hanyar boye shi cikin wasu magunguna ko kayan kasashen ketare da ake shigo da su kasar ta Ghana.

Ko a watan da ya gabata saida hukumar kula da shige da fice ta kasar Ghana ta bayyana cewar ba zata dauki mata masu bilicin aiki ba saboda dalilai na kiwon lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng