Taron manya: taron majalisar koli na jam’iyyar APC ya samu halartar masu ruwa da tsaki
A ranar Talata 27 ga watan Feburairu ne shuwagabannin jam’iyyar APC suka halarci taron majalisar koli na jam’iyyar wanda uwar jam’iyyar ta shirya, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A yayin jawabinsa, shugaba Buhari ya zayyano duk nasarorin da ya gwamnatinsa ta samu, amma yace ba zai yi kasa a gwiwa ba duk da cewa manyan zabuka na karatowa, don haka ya bukaci yayan jam’iyyar su hada kai, kuma a ayi aiki tare don cigaba jam’iyya duk da bambamce bambancen dake tsakaninsu.
KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC
Da wannan ne shugaba Buhari ya nemi dukkanin yayan jam’iyyar su baiwa kwamitin sulhu dake karkashin jagorancin Asiwaju Ahmad Bola Tinubu don yin aikinsa yadda ya kamata, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito
Daga karshe shugaba Buhari ya tabbatar da cewa yana sane da cewa gwamnatinsa bata kammala biyan bukatun yan Najeriya ba, da ma na yayan jam’iyyar, sai dai yace gwamnatinsa na ta kokarin shawon matsalolin da suka addabi Najeriya.
A wani labarin kuma, rahotanni sun tabbatar ba’a hangi keyar shugaban majalisar dattawa ba a wajen taron, Sanata Abubakar Bukola Saraki, wanda hakan ya sa ake ganin ko dai rikicin jam’iyyar bai kau bane.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng