Shugaban rundunar sojin sama ya koma jihar Yobe domin ceto 'yan matan Dapchi da aka sace
- Rundunar Sojin saman Najeriya ta koma jihar Yobe domin ceto 'yan matan Dapchi
- Ranar Litinin dinnan ne 26 ga watan Fabrairun wannan shekarar, rundunar sojan saman ta baza dakarun ta ko ina a yankin domin nemo inda yan matan suke
A yau ne Shugaban rundunar sojan saman Najeriya CAS Abubakar Sadique, ya koma jihar Yobe domin daukan kwakkwaran mataki akan neman daliban da aka sace a garin Dapchi.
DUBA WANNAN: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC
Ba a jima ba rundunar sojan saman Najeriyan dama sauran hukumomin tsaro suka tura dakarun su yankin arewa maso gabas domin ceto yan matan da aka sace.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin dinnan ne 26 ga watan Fabrairun wannan shekarar, rundunar sojan saman ta baza dakarun ta ko ina a yankin domin nemo inda yan matan suke.
A kwanakin baya majiyar mu Legit.ng ta kawo muku rahoton sace yan matan da aka yi a makarantar sakandaren mata dake garin Dapchi. Abinda ya dinga kawo cece kuce a kafafen yada labarai na kasar nan. Har ya zuwa wannan lokacin dai babu labarin halin da suke ciki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng