Ma'aurata sun sha bulala a bainar jama'a saboda yin aure babu yardar iyayen su
- Dakarun Taliban sun yiwa wasu ma'aurata bulala a bainar jama'a saboda sun yi aure babu yardar iyayen su
- Ma'auratan 'yan asalin kasar Afghanistan sun gudu zuwa yankin Ghor dake yammacin kasar inda su ka yi aure
- Ko a ranar 14 ga watan nan saida 'yan Taliban din su ka jefe wani matashi bisa zargin sa da yin zina
Dakarun Taliban sun yiwa wani matashi da wata matashiya bulala a bainar jama'a saboda sun yi aure ba tare da iyayen su sun amince ba.
Matasan sun gudu daga garin Faryab dake arewacin kasar Afghanistan zuwa yankin Ghor dake yammacin kasar inda su ka yi auren su.
Jami'in kungiyar Taliban, Yurish, ya shaidawa kamfanin labarai na dpa cewar "a ranar Litinin da yamma dakarun Taliban su ka yi hukuncin bulala ga matasan da su ka yi aure ba tare da yardar iyayen su ba."
Lamarin ya faru ne a yankin Bandar dake karkashin ikon 'yan Taliban a kasar Afghanistan.
Matasan sun gudu ne saboda iyayen su sun ki amincewa su yi aure duk kaunar da su ke yiwa junan su.
Tun bayan samun karin karfin kungiyar Taliban ake samun yawaitar alkalan dakali dake yin hukunci yadda su ke so a kan jama'a.
KARANTA WANNAN: An fitar da kididdigar ta'annacin da kungiyar Boko Haram ta yi a kasar kamaru cikin shekarar 2017
A cewar kasar Amurka, kashi 13% cikin 100% na kasar Afghanistan na karkashin ikon Taliban.
Ko a ranar 14 ga watan nan saida 'yan Taliban su ka jefe wani matashi bisa zargin sa da aikata laifin zina a yankin Sar-e-Pul dake arewacin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng