Basabamba: Yadda wani mutumi ya angwance da amare guda biyu a rana daya

Basabamba: Yadda wani mutumi ya angwance da amare guda biyu a rana daya

Wata sabuwa inji yan caca, wannan shi ne lamarin da ya auku a karshen makon daya gabata, inda wani matashi ya nuna kwarewarsa wajen iya neman aure, wanda hakan ya baiwa kowa mamaki.

Shi dai wannan matashin ango da ba fayyace sunansa ba, ya tari aradu da ka ne, ko kuma a ce ya dauki dala ba gammo, inda ya auri wasu tsala tsalan yan mata guda biyu a lokaci daya, kamar yadda Legit.ng ta gano.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Basabamba: Yadda wani mutumi ya angwance da amare guda biyu a rana daya
Ango da Amare

An sha wannan shagali ne a garin Abiriba na jihar Anambra, inda jama’a daga sassan jihar suka halarci bikin don kashe kwarkwatan idanuwansu, wai kada ka bari a baka labari, inji Hausawa.

Sai dai, dalilin da yasa wannan aure ya baiwa jama’a mamaki shi ne, ba’a san mabiya addinin kirista da auren matar aure fiye da guda daya ba, musamman inyamurai, wanda da dama daga cikinsu mabiya darikar katolika ne.

A wani labarin kuma, an samu wani matashi Musulmi, da shi ma ya auri yan mata guda biyu a rana daya, a jihar Nassarawa. A nan sai mu ce Allah ya taimaki masu niyyar aure da nufin raya sunnah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng