An fitar da kididdigar harin da kungiyar Boko Haram ta kamaru a 2017

An fitar da kididdigar harin da kungiyar Boko Haram ta kamaru a 2017

- Wata kididdiga ta tabbatar da kungiyar agaji ta majalisar dinkin duniya ta gudanar ta tabbatar da cewar sau 60 kungiyar Boko Haram ta kai harin kunar bakin wake a kasar Kamaru

- Sakatariyar kungiyar, Ursula Mueller, ta sanar da hakan yayin wata ziyara ta kwanaki biyu da ta kai kasar Chadi

- Kasar Kamaru ce ta fi samun matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram bayan sun fuskanci matsin lamba daga Sojin Najeriya

Wata kungiyar majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewar sau 60 kungiyar Boko Haram ta kai harin kunar bakin wake a kasar Kamaru cikin shekarar 2017.

Sakatariyar kungiyar, Ursula Mueller, ce ta sanar da hakan yayin wata ziyara ta kwanaki biyu da ta kai kasar Chadi.

Mueller na kasar ta Chadi ne domin yin kiyasin karancin aiyukan kungiyoyin jin kai da matsalolin karancin cigaba da kasar ke fuskanta.

An fitar da kididdigar harin da kungiyar Boko Haram ta kamaru a 2017
Sojin kasar kamaru

Ta bayyana cewar kasar Kamaru ce tafi fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram bayan da mayakan ta su ka fuskanci matsin lamba daga sojin Najeriya.

"A shekarar 2017, kungiyar Boko Haram ta kai harin kunar bakin wake sau 60 a Kamaru, adadin da ya karu da kaso 50% a kan hare-haren da kungiyar ta kai kasar a shekarar 2016," a cewar Mueller.

Ta cigaba da cewa, "kimanin mutane miliyan 3.3 na bukatar taimakon gaggawa a kasar Kamaru. A kuryar kudancin kasar, duk mutum daya cikin mutane uku na fuskantar matsanancin halin yunwa."

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace dan gani-kashenin jam'iyyar APC a Bayelsa

Ta bayyana adadin tallafin kungiyoyin agaji da cewar ya yi kadan kasar.

Ana saka ran Mueller zata gana mahukuntan kasar Chadi domin tattauna matsalolin aiyukan jin kai da kasar ke fuskanta domin ganin yadda za su hada karfi da karfe.

Kafin zuwan ta kasar Chadi, Mueller, ta ziyarci kasar Kamaru inda ta yi kira ga kungiyoyin agaji da su kawo wa kasar ta Kamaru agaji tare da yin wani kira ga gwamnatin kasar da ta rubanya aiyukan taimako a yankin da abin ya fi shafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng