Babban dalilin da ya haɗa Musulmai da Kirista faɗa a jihar Kaduna har aka yi asarar rayuka da dukiyoy

Babban dalilin da ya haɗa Musulmai da Kirista faɗa a jihar Kaduna har aka yi asarar rayuka da dukiyoy

A jiya, Litinin, 26 ga watan Feburairu ne wata rikici ta kacame tsakanin mazauna garin, Muslmai da Kirista garin Kasuwar Magani, dake cikin karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.

Binciken Legit.ng ya binciko musabbabin wannan kazamin rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, kamar yadda Yansanda suka tabbatar, da kuma gidaje d dama, dalilin kuwa shi ne sauya addini da wata budurwa kirista ta yi, zuwa Musulunci.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Wannan musulunta da budurwar ta yi bai yi ma yan uwanta dadi ba, inda suka nuna bacin ransu, tare da tilasta mata dole sai ta koma addinin Kirista, nan da nan ita kuma ta tattara inata inata ta gudu daga gidan.

Ashe wannan abu bai tsaya nan ba, sai kiristocin garin suka bukaci duk wata mace kirista dake aure a gidan Musulmi ta fita ba tare da bata lokaci ba, ko kuma su da kansu zasu fitar da ita, haka zalika sun gargadi yayansu mata dake soyayya da musulmai su daina gaba daya.

Daga nan ne fa sai rikici ya kacame tsakaninsu da Musulman garin, inda kafin kowa ya Ankara an halaka mutum 12 da kona gidaje, ciki har da gidan wani mutumi mai suna Mista Joshua Zango, wanda yace an kona gidansa, motoci guda 2, babur, kajinsa da yake kiwo, hatsin da suka noma, da kuma shagon mamansu.

Zuwa yanzu dai hankula sun kwanta, bayan gwamnati ta aike da jami’an tsaro da zasu magance rikice rikicen, sa’annan gwamnati ta umarci a bincike duk masu hannu cikin rikicin da zummar gurfanar da su gaban kuliya manta sabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng