Gwamnatin tarayya ta ba da sabon umarni akan sigar da za a rika kira Buhari da shi a wurin taro
- Sakataren gwamnatin tarayya ya ce ba dai-dai bane a rika kiran Buhari da sigar Janar a wurin taro
- Boss Mustapha ya ce da sigar “SHUGABAN KASAR NAJERIYA, MUHAMMADU BUHARI ya kamata a rika kiran Buhari a wurin taro
Gwamnatin Tarayya ta bayar da sabon umarnin akan sigar da za a rika kira sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a da shi a wurin taro.
A wata madauwari da sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Gida Mustapha, ya aikawa duka Ma’aikatun kasar, yace shugaba Buhari, tsohon soja ne da yayi ritaya a mukamin Manjo Janar, saboda haka bai daidai bane yanzu da ya zama shugaban kasa a mulkin farar hula a cigaba da kiran sa da sigar mukamin sa na soja a wurin taro.
A madauwari da ya aika wa ma’aikatun kasar, Boss yace, da ga yanzu za a rika kiran Buhari da sigar, 'SHUGABAN KASAR NAJERIYA, MUHAMMADU BUHARI.'
“Daga yanzu za a rika kiran Buhari da sigar, 'SHUGABAN KASAR NAJERIYA, MUHAMMADU BUHARI ,' a taron sojoji ne kadai za a iya kiran shi da sigar Janar," Inji Mustapha.
KU KARANTA : Ba zan yi kasa a guiwa wajen kare Buhari ba- Abdullahi Adamu
Daga karshe yayi kira da ma’aikata sun yi aiki da wannan sabon umarni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng