Dakarun sojin Nigeria da na Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram 35 - Kanal Onyema Nwachukwu
- Dakarun sojin Nigeria da na Kamaru 'sun samu nasarar kashe mayakan Boko Harm 35
- Sojoji sun ceto farar hula guda 194 da Boko Harm sukayi garkuwa da su inji Kanal Onyema
Dakarun sojojin Najeriya dake attisayen Lafiya Dole, ta ce dakarun sojin ta da na Kamaru sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram guda35.
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanal Onyema Nwachukwu, ya fadawa manema labaru cewa al’amarin ya faru ne tsuburan da ke yankin Chadi da kuma yankin Sambisa a ranar Litinin.
A cewar sa, dakarun sun kai wa kauyukan da mayakan Boko Haram suke buya sammame irin su Kusha-Kucha, Surdewala, Alkanerik, Magdewerne da kuma Mayen, wadanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka kashe mayaka 35 sannan suka kwace bindigogi 15 daga wurinsu.
KU KARANTA : Ba zan yi kasa a guiwa wajen kare Buhari ba- Abdullahi Adamu
Kanal Onyema Nwachukwu, ya kara da cewa, sojojin sun ceto farar hula guda 194 da aka yi garkuwa da su a kauyakan
Bayan haka sojojin sun rusa duka gidajen wucin gadin da mayakan Boko Haram suka gina a kauyukan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng