Sarki Salman ya kori manyan hafsoshin rundunar sojin Saudiyya

Sarki Salman ya kori manyan hafsoshin rundunar sojin Saudiyya

- Sarki Salman ya kori duka manyan hafsoshin rundunar sojin kasar Saudi

- Saudiyya ba ta bayyana dalilin yasa ta sauki hafsoshin rundunar sojin Saudiyya

Masarautar Kasar Saudiyya ta sallami duka hafsoshin rundunar sojinta, ciki har da shugaban shugaban ma'aikatan kasar.

Sarki Salman ya dauki wannan mataki a cikin tsakar daren ranar Litinin

Kamfanin dillancin labaran kasar ne ta wallafa jerin sunayen mutanen da aka kora, amma ba ta bayyana dalilin korar ba.

Sarki Salman ya kori manyan hafsoshin rundunar sojin Saudiyya
Sarki Salman ya kori manyan hafsoshin rundunar sojin Saudiyya

Lamarin na faruwa ne a lokacin da yakin da ake yi a kasar Yaman, inda kasar Saudiyya ta ke jagorantar rundunar gamayyar wasu kasashen labarawa wajen yakar ‘yan tawayen kabilar Houthi.

KU KARANTA : Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja

Wannan shine shekara ta uku da kasar Saudiyya ke yaki da ‘yan tawayen kabilar Houthi dake kasar Yaman .

An yi amannar cewar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda shi ne ministan tsaron kasar, yasa aka gudanar da wannan sauye-sauye a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng