Satar 'yan matan Dapchi: Rundunar sojoji sun dorawa 'yan sanda laifi
Kawo yanzu dai labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa jami'an rundunar sojin Najeriya sun dora alhakin sace 'yan matan Dapchi da aka yi a cikin satin da ya gabata a dalilin sakacin 'yan sandan Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar ta sojoji dake yaki da 'yan ta'addan a yankin arewa maso gabas ta 'Operation Lafiya Dole' Kanal Onyeama Nwachukwu shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Maiduguri.
KU KARANTA: An kama dan Boko Haram a jihar Ekiti
Legit.ng ta samu cewa haka zalika Kanal Onyeama ya bayyana cewa zargin jami'an su da Gwamnan yayi sam bai dace ba don kuwa kafin su fice daga farfajiyar makarantar sai da suka mika ragamar kula da ita ga 'yan sandan Najeriya.
A wani labarin kuma, kawo yanzu dai an tabbatar da akalla rabin 'yan matan da aka sace a makarantar koyon fasaha da kere-kere da ke a garin Dapchi, jihar Yobe suna a wani kauye cikin jamhuriyar Nijer.
Kamar dai yadda muka samu, wasu da ke da masaniya kan lamarin sun shaidawa kamfanin jaridar Daily Trust cewa an raba 'yan matan ne da aka sace zuwa kashi biyu inda aka tafi da kashi daya ya zuwa wani daji a jihar Borno, dayan kuma aka tafi da shi Nijer.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng