Shahararren mai kudin nan na duniya Bill Gates ya shawarci attajiran Najeriya game da kyauta
Fitaccen attajirin nan na duniya da kuma yayi fice wajen taimakon bayin Allah mai suna Bill Gates ya shawarci daukacin attajirai da masu hannu da shunin Najeriya da su rika taimakawa marasa karfi a cikin al'ummar su.
Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu, yana kun she ne a cikin jawabin da shi Bill Gate din yayi yayin da yake tattaunawa da gidan jaridar Daily Trust inda yayi karin haske game da ayyukan taimakon da yake yi.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa gwamnonin APC ke son Buhari yayi tazarce
Legit.ng ta samu cewa Bill Gates din da ke zaman shugaban kamfanin kera kwamfutocin nan na Microsoft ya kuma jinjinawa attajirin nan dan asalin Najeriya daga jihar Kano watau Aliko Dangote bisa irin yadda ya dukufa wajen saukaka rayuwar masara karfi a Nahiyar ta Afrika.
A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja kuma daya daga cikin manyan dattawan arewa mai suna Janar Yakubu Gowon da safiyar yau ya jagorancin sauran mambobin wata kungiya dake yi wa kasa addu'a mai suna 'Nigeria Prays' a zuwa jihar Borno, garin Maiduguri.
Kamar yadda muka samu, gwamnan jihar ta Borno, Alhaji Kashim Shettima shi ne ya tarbi tsohon shugaban kasar sannan kuma yayi masa addu'ar samun nasara.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng