Wani kasurgumin dan Boko Haram ya shiga hannu bayan ya kashe dan sanda a jihar Ekiti
Wani kasurgumin dan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram yanzu haka yana gidan yari bayan da kotu ta tasa keyar sa bisa zargin da take yi masa na kashe dan sanda a jihar Ekiti dake a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Dan Boko Haram din dai da ya bayyana kan sa da sunan Abdulsalam Adinoyi ya shiga hannu ne sannan kuma aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare ta garin Ado Ekiti, babban birnin jihar ta Ekiti.
KU KARANTA: Tsarin zaben 2019: Ba gudu ba ja da baya - INEC
Legit.ng dai har ila yau ta bankado cewa shekarun wanda ake zargin 36 a duniya sannan kuma ya kashe wani karamin dan sanda ne mai matsayin Sajent mai suna Gana Jiya dake a bakin aikin sa a karamar hukumar Oye-Ekiti.
A wani labarin kuma, Biyo bayan mummunan al'amarin da ya auku a satin da ya gabata inda aka ruwaito wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai a makarantar 'yan mata ta kwana dake a garin Dapchi, jihar Yobe inda kuma har aka sace wasu matan masu yawa, an shawarci gwamnatoci da su rufe makarantun kwana.
Wannan dai mun samu daga wani bawan Allah dake rajin tabbatar da adalci da kuma tabbatacen zaman lafiya mai suna Malam Alfaruk wanda ya bayar da wannan shawarar a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng