Gwamna Gaidam ya bayar da aiki kyauta ga zakakuran dalibai
- Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya saka wa wasu zakakuran daliban jihar Yobe da aiki kyauta
- Jami'ar jihar Yobe ta bayar da digirin girmamawa ga gwamna Ibrahim Gaidam
- Shugaban jami'ar jihar Yobe, Farfesa Yakubu Mukhtar, ya bayyana cewar jami'ar, karkashin gwamnatin Ibrahim Gaidam, na samun cigaba matuka
Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam, ya karrama wasu zakakuran dalibai da su ka kammala karatu a jami'ar jihar da sakamakon kece raini.
Gwamna Gaidam ya sanar da haka ne yayin da ya halarci bikin yaye daliban jami'ar jiya a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Jami'ar jihar Yobe ta yaye dalibai 2,290 da suka fara karatu a zangon 2012/2013. Mutum 38 ne daga cikin adadin daliban su ka fita da sakamako mai daraja ta farko.
Gaidam ya bayyana cewar gwamnatin sa zata cigaba da bayar da gudunmawa ga jami'ar da ma bangaren ilimi bakidaya ta hanyar ware masu kaso mafi tsoka a kasafin kudin jihar.
KU KARANTA: Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja
Kazalika hukumar jami'ar ta girmama gwamna Gaidam da digirin girmamawa.
A nasa bangaren, shugaban jami'ar, Farfesa Yakubu Mukhtar, ya yabawa gwamna Geidam bisa irin gudunmawar da yake bawa jami'ar tare da bayyana cewar ta samu cigaba sosai karkashin mulkin gwamna Gaidam.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng