Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja

Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja

- Wata kotun Abuja ta bayar da umarnin tsare wani mutum, Abdulkarim Dayyabu, mai shekaru 28 a kurkuku

- Ana tuhumar mutumin ne da kisan wani yaro, Umaru Hussaini, ta hanyar daddatsa shi da adda

- Dan sanda mai gabatar da kara, Simon Lough, ya shaidawa kotu cewar Zubairu ya aikata laifin ne ranar 1 ga Oktoba shekarar 2013

Wata kotun Abuja dake Abuja ta bayar da umarnin tsare wani mutum, Abdulkarim Dayyabu, mai shekaru 28 a gidan yari na kuje bayan samun sa da laifin kashe wani yaro, Umaru Hussaini, mai shekaru 13.

Zubairu, mazaunin unguwar kauyen Pangu dake Kwali, Abuja, na fuskantar tuhumar aikata laifin kisan kai, laifin da ya ce sam bai aikata ba.

Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja
Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja

Dan sanda mai gabatar da kara, Simon Lough, ya shaidawa kotun cewar Wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2013.

Lalough ya ce Zubairu ya yi amfani da adda mai kaifi ya datse hannun Hussaini bayan musu ya kaure tsakanin su.

KARANTA WANNAN: 'Yan sanda sun yi caraf da wasu 'yan fashi bayan motar su ta yi hatsari

Ya kara da cewar zubar jini daga saran ya yi sanadin mutuwar Hussaini. Kazalika ya ce hukumar 'yan sanda ya samu addar a wurin da ya aikata laifin.

Alkalin kotun, Bolaji Belgore, ya daga sauraron karar ya zuwa 13 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng