Dalilai 3 da yasa matasa bazasu iya kwace mulkin kasar a 2019 ba
A halin da ake ciki a yanzu hankulan mafi akasarin mutanen Najeriya ya koma kan yadda zaben 2019 zai kasance.
Matasa da dama sun nuna ra’ayinsu na son ganin an ba matasa damar da za’a dama dasu a harkar siyasar kasar musamman ganin yadda tsofaffi ne ke rike da kusan dukkan mukaman gwamnati.
Sai dai duk da haka akwai masu kokwanto da kamun ludayin matasa ta fannin shugabancin kasar. Haka zalika su kansu matasan basu da cikakken kwarin gwiwa na yin takara.
Ga wasu daga cikin abubuwan da zasu zamo kalubale ga matasa a zaben 2019:
1. Matasa basu goya ma junansu baya sakamakon ba sa siyasa in ba da kudi ba, saboda haka mafi akasarin matasan kasar yan abi yarima a sha kida ne, duk gurin da kudi yake nan suke. Wannan na daga cikin kalubalan da matasa ka iya fuskanta a zaben 2019.
2. Wani dalili da zai sake sa matasa rashin kai labari a 2019 shine ganin cewa tsofaffi ne suka saba mulkar kasar, hakan ya sa an raina matasa inda ake ganin idan har tsoho zai gaza ko ya fuskanci matsala a wajen mulkar kasar, toh shi matashi a wad a zai iya?, wannan yasa mutane bazasu ba matasan cikakken goyon bayan da ya dace ba.
KU KARANTA KUMA: Ina maka fatan karin shekaru cikin koshin lafiya – Jonathan ya jinjinawa Shagari yayinda ya cika shekaru 93
3. Daga karshe son zuciya da kwadayin tara abun duniya ya zamo babban cikas ga matasan wannan zamani, domin basu da wani buri day a wuce suga sun tara abun duniya, saboda haka mutane ke ganin koda an basu dama babu wani abun arziki da zasu tabuka wa al’umman kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng