Hujjoji: Addinin musulunci ya yiwa Kiristanci fintinkau, a cewar Bishop Sam Zuga

Hujjoji: Addinin musulunci ya yiwa Kiristanci fintinkau, a cewar Bishop Sam Zuga

Wani malamin addinin Kirista, Bishop Sam Zuga, ya bayyana cewar addinin musulunci gaba yake da na Kiristanci bisa dogaro da wasu hujjoji.

Malamin addinin ya bayar da hujjojin kamar haka:

An haifi Annabi Isa (AS) shekaru 571 kafin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) amma duk da haka addinin musulunci na goga kafada da Kiristanci a duniya.

Musulumi na amsa sunan Mohammed fiye da Kiristoci dake amsa sunan Emmanuel.

Musulumi na yin sallah biyar a rana amma da kyar kiristoci ke zuwa coci sau daya a sati.

Ya kara da cewar Qur'an guda daya ne kuma cikin yare guda amma littafin injila (bibble) ya fi kashi 10 a cikin yaren Turanci kadai.

Hujjoji: Addinin musulunci ya yiwa Kiristanci fintinkau, a cewar Bishop Sam Zuga
Bishop Sam Zuga

Musulumi kan iya yin sallah a kowanne masallaci kuma a ko ina amma mabiya addinin Kirista ba zasu soma shiga wata cocin ba saboda ba a irinta su ke ibada ba.

Idan har karbi addinin musulunci, babu mai tambayar ka masallacin ka, amma idan mutum ya zama Kirista dole sai ya zabi coci ko kuma ka tashi a tutar babu.

Musulumi sun fi kiristoci saukin kai domin sun sha halartar tararruka na a garin Gboko, jihar Benuwe, wani abu da Kiristoci ba zasu iya ba.

Hujjoji: Addinin musulunci ya yiwa Kiristanci fintinkau, a cewar Bishop Sam Zuga
Bishop Sam Zuga

Akwai yarda wurin musulmi domin da zarar mutum ya karbi addinin musulunci zaka ga kowa na son taimakon shi.

Bishop Zuga ya kara da cewar babu rarrabuwar kai tsakanin musulmi kamar yadda ake samu a Kiristanci domin idan ba ka yi bincike ko ka zauna da musulmi ba, ba lallai ka san akwai rabuwar kai tsakaninsu ba.

KARANTA WANNAN: Igiyar leko ta hallaka uwa da 'ya'yan ta hudu a Maiduguri

Idan musulmi na azumi duk duniya sai ta sani kuma baka jin labarin samun limaman bogi kamar yadda ake samu cikin malaman addinin Kirista.

Musulumi basa musu da limaman su kamar yadda kiristoci ke musu da karyata limaman su, sannan uwa uba ga hadin kai wurin musulmi.

Bishop Zuga, dan asalin jihar Benuwe, ya rufe da cewar, babu wani musulmi da bai yarda da annabtar annabi isa ba, amma abin mamaki babu kiristan da ya yarda da Annabi Muhammadu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng