Aiki ya kwana: Ma’aikatan shari’a sun yi ma Alkalin Alkalai tutsu a jihar Nassarawa
Yayan kungiyar ma’aikatan shari’a, JUSUN reshen jihar Nassarawa, sun hana Alkalin Alkalai na jihar, Mai shari’a Suleiman Dikko shiga ofishinsa a yayin da ya tafi wajen aiki da safiyar ranar litinin.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito yayan kungiyar sun shiga yajin aiki ne tun a ranar 16 ga watan Feburairu kan wasu bukatun da suke gwagwarmaya akansu, da suka hada da rashin karin girma, karin albashi da kuma rashin rantsar da kwararrun jami’ansu a matsayin Alkalai.
KU KARANTA: IBB da Obasanjo na bakin ciki da nasarorin da Buhari ya samu ne – Sanata Kurfi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito da kyar da sudin goshi yayan kungiyar suka bude ma Alkalin Alkalan kofarsa, bayan ya kwashi tsawon lokaci yana yi musu magiya, daga nan kuma shugaban JUSUN, Jimoh Musa ya tabbatar da burinsu na cigaba da yajin aiki har sai baba ta ji, don neman hakkokinsu.
Sai dai a hannu guda, Alkalin Alkalan jihar ya umarci dukkanin ma’aikatan sashin shari’ar da su koma bakin aiki, ko kuma a dakatar da albashinsu;
“Duk ma’aikacin da bai koma bakin aiki ba, ba za’a biya shi albashin lokuttan da ya kwashe yana yajin aiki ba.” Inji Kaakakin babban kotun jihar, Enoch Ali-Maku.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng