Jami’an hukumar kwastam suna sumogan shinkafa da motoci a farashin N30,000 a iyakokin kasar
- Bincike ya nuna jam'ian hukumar kwastam suna taya 'yan sumoga shigowa da haratattun kaya cikin Najeriya
- 'Yan sumoga suna biyan jami'an kwastam N30,000 su shigo musu da haramtattun kaya cikin Najeriya
Legit.ng ta samu rahoton cewa jami’an hukumar fasakwabri (Kwastam) da ya kamata su rika hana mutane wucewa da haramtattun kaya a iyakokin Najeriya, suke ta ya ‘yan sumoga shigowa da motoci da shnikafa cikin kasar
Idan aka tuna baya gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da shinka kasar waje da motoci cikin kasar ta iyakokin ta.
Amma tunda gwamnati ta sanya wannan dokar, yan sumoga sun samar da wata sabuwar hanyar shigowa da motoci da sauran haramtattun kaya cikin kasar.
‘Yan sumoga suna amfani da jami’an hukumar kwastam ne dake iyakokin kasar wajen shigo musu da haramtattun kayayyaki cikin kasar.
KU KARANTA : 'Yan matan Dapchi : Iyaye sun ki amincewa da adadin ‘yan matan da gwamnati ta ce an sace
Rohatanni sun nuna ‘yan sumoga suna biyan jami’an kwastam N30,000 su shigo musu da haramtattun kaya cikin Najeriya kamar shinkafa da motoci daga jamhuriyyar Benin.
A wani gagarumin bincike da aka gudanar a iyakokin Najeriya, shugaban hukumar kwastam Kanal Hameed Ali, ya ba da umarnin sallamar wasu jami’an hukumar kwastam na reshen jihar Ogun guda biyu bayan an kama su da laifm shigowa da haramtattun kaya daga jamhuriyya Benin zuwa cikin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng