'Yan matan Dapchi : Iyaye sun ki amincewa da adadin ‘yan matan da gwamnati ta ce an sace
- Ministan watsa labaru da al’adu Lai yaziyarci jihar Yobe a ranar Lahadi
- Lai Mohammed yayi ganawar sirri da jami'an tsaro da iyayen 'yan matan da aka sace a GSS Dapchi
Cacar baki ya barke tsakanin gangamin iyayen ‘yan matan Dapchi da aka sace da gwamnatin tarayya akan adadin ‘yan matan da suka bace.
Ministan watsa labaru da al’adu Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya zata fara neman ‘yan mata 110 da aka sace daga cikin ‘yan mata 906 dake makaranatar GSS Dapchi.
Lai Mohammed, ya bayyana haka a lokacin da yake zanatwa da manema labaru, bayan ya kammala ganawar sirri da jami’an tsaro a ranar Lahadi a jihar Yobe.
KU KARANTA : Najeriya: Makiyaya sun tashi dan mallakar katin zabe
Yace gangamin iyayen matan da aka sace sun halarci taron inda ya ce ‘yan mata 110 sun bace.
Amma iyayaen matan sun ce basu da wata masaniya akan ziyarar jihar Yobe da Ministan yayi kuma adadin matan da y ace sun bace bah aka bane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng