Dubban yan APC na kudancin Najeriya za su shirya babban gangamin goyon bayan Buhari
- Dubban yan APC na kudancin Najeriya za su shirya babban gangamin goyon bayan Buhari
- An yi wa gangamin lakabi da “National Unity and Solidarity Rally”
- Babban sakataren gudanarwar jam'iyyar na shiyyar Mista Paul Obi shine ya sanar da hakan
Wasu gungun dubban magoya bayan jam'iyya mai mulki ta APC a yankin kudu maso kudancin Najeriya ya zuwa yanzu sun yi nisa a cikin wani shirin su na gudanar da wani babban gangamin nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari da suka yi wa lakabi da “National Unity and Solidarity Rally”.

KU KARANTA: An gano inda rabin yan matan Dapchi suke
Babban sakataren gudanarwar jam'iyyar na shiyyar Mista Paul Obi shine ya sanar da hakan ga duniya inda yace suna mika gayyatar su zuwa ga dukkan masu kaunar shugaban daga kowane lungu da sako na yankin su fito domin yin gangamin.
Legit.ng ta samu cewa Mista Obi ya bayyana cewa wannan dai wata dama ce da yankin da kuma yan yankin za suyi anfani da ita wajen nunawa duniya irin kaunar su ga shugaba Buhari.
A wani labarin kuma, fadar shugaban kasar Najeriya dake a unguwar Villa, babban birnin tarayya Abuja ta bayyana a jiya cewa su fa su shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo batun zarcewa bisa mulki a zaben 2019 ma bai dame su ba.
A maimakon hakan, kamar yadda muka samu daga fadar, an bayyana cewa su shugabannin kawo yanzu ba abun da ke a ran su irin tabbatar da samun cigaba mai dorewa a kasar tare kuma da jin dadin 'yan Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng