Gamji dan kwarai: Yadda ta kwashe tsakanin Ahmadu Ali da Sardauna a lokacin da aka sallami daliban Arewa daga jama’ar Ibadan
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmadu Ali ya bada labarin yadda tsohon firimiyan yankin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya mayar da daliban Arewa makaranta, bayan an sallame su daga jami’ar Ibadan.
Ahmadu Ali ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Daily Trust, inda yace a zamanin da yake dalibi a jami’ar Ibadan, shi ne sakataren kungiyar daliban Najeriya gaba daya, inda yace sun shiga matsala da hukumomin jami’ar, wanda ya sa aka sallami duk daliban makarantar gaba daya.
KU KARANTA: Jama’a ayi hattara: Wani ma’aikacin banki ya aikata ma wani abokin hurdarsu halin bera
Daga cikin sharuddan da hukumar jami’ar ta gindaya ma kowani dalibi shi ne sai ya kawo takarda daga iyayensa dake tabbatar da cewa ba zai sake aikata laifi a makarantar ba, har ya kammala karatunsa, sai dai Ali yace daliban basu amince ba.
Duk da haka sai hukumar ta sanya Yansanda suka fatattakesu daga makarantar, ga shi basu da ko sisi, har yasa daliban Arewa dake jami’ar suka tare wata babbar motar daukan kaya, ta kai su Kaduna, daga nan Sardauna ya samu labarin sallamar ta su.
Bayan kwana biyu ne Sardauna ya sa aka kira masa Ali, inda ya tambaye shi laifin da suka aikata da har ya sa aka sallame su daga makarantar, sa’annan ya nuna bacin ransa game da yadda aka sallamo yan Arewa.
“Mun tura ku kuyi karatu ne, amma sai kuka je kuna farfasa musu kofofi da tagogi. Ba abinda muka tura ku jami’ar Ibandan yi ba kenan” Inji Sardauna, sa’nnan ya umarce su da su je su rubutar wasikar ‘ba zan kara ba’ ga makarantar, amma a nan ma daliban suka ki.
Ashe bayan tafiyan daliban ARewa, sai aka bude ma dalibhttps://www.facebook.com/naijcomhausaan kudanci su koma makarantar don cigaba da karatu, daga nan ne Ahmadu Ali ya sake komawa wajen Sardauna, inda ya basu takardar da jami’ar ta bukaci iyaye su rubuta.
“Ba tare da bata lokaci ba hukumar jami’ar ta mayar da mu, bayan mun kai musu takarda daga Sardauna.” Inji Ahmadu Ali.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng