Da dumin sa: An gano inda rabin 'yan matan makarantar Dapchi da aka sace suke
Kamar yadda muka samu dai daga majiyar mu, kawo yanzu dai an tabbatar da akalla rabin 'yan matan da aka sace a makarantar koyon fasaha da kere-kere da ke a garin Dapchi, jihar Yobe suna a wani kauye cikin jamhuriyar Nijer.
Kamar dai yadda muka samu, wasu da ke da masaniya kan lamarin sun shaidawa kamfanin jaridar Daily Trust cewa an raba 'yan matan ne da aka sace zuwa kashi biyu inda aka tafi da kashi daya ya zuwa wani daji a jihar Borno, dayan kuma aka tafi da shi Nijer.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa bangaren kungiyar Boko Haram din ne da ke biyayya ga dan tawaye Musab Albarnawi ne suka sace matan ba bangaren Shekau ba.
Kawo yazu dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa 'yan ta'adda sun shiga wata makarantar kwana ta garin Dapchi dake a jihar Yobe inda kuma suka yi awon gaba da 'yan mata akalla 110.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar labarai da ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya fitar a ofishin sa jiya Lahadi inda kuma ya tabbatar da cewa yanzu haka gwamnati ta kara daura damara don kwato 'yan matan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng