Gabas ta Tsakiya: An cimma tsagaita wuta a yakin da ake yi a Siriya

Gabas ta Tsakiya: An cimma tsagaita wuta a yakin da ake yi a Siriya

- Shekaru bakwai ana gwabza yakin baasasa a Siria

- Kasar ta ruguje gaba dayanta

- An kira majalisar dinkin duniya ta sasanta

Gabas ta Tsakiya: An cimma tsagaita wuta a yakin da ake yi a Siriya
Gabas ta Tsakiya: An cimma tsagaita wuta a yakin da ake yi a Siriya

A yakin da masu tawaye keyi na kokarin kawar da Mulkin Basshar Al-Asad na kasar Siriwa watau Sham, wanda yaki ci yaki cinye wa, har mutanen kasar miliyan uku sun tsere, wasu biliyan sun mutu, wasu kuma sun tagayyara.

A yanzu dai majalisar dinkin duniya ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan da aka shiga mako na biyu ana gwabzawa tsakanin mayakan tawayen da na gwamnati a garuruwan da suka rage ba'a kwato su ba.

Rikicin Siriyar dai ya zamo wani babban kalubale ga kasashen duniya, nda suka rasa wa zasu mayar saniyar ware wa zasu baiwa gaskiya, ganin cewa Basshar din da basu so shine kuma mai saukin ra'ayi, su kuma sauran mayakan sun zamo yan ta'adda.

DUBA WANNAN: Biyan miliyoyi da ake yi wa Boko Haram ya sasu sace matan Dapchi

Kasar ta Siriya dai na hannun kasashen Rasha da Iran ne, wadanda suka aikaa Hezbolla domin taimakawa Assad. A gefe guda kuma makwabta larabawa ke mara wa sauran yan tawaye baya.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniiya dai a yanzu ya cimma matsaya da masu fada aji na kasar domin a tsagaita wuta a daina sakin bam daga sama inda yake kashe mutane a gidajensu. Ana sa rai agaji zai kai ga wadanda fadan ya rutsa dasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng