Sojin Saman Najeriya sun yi aikin agaji a sansanonin 'yan gudun hijira
- Bayan yaki, akwai kuma agaji da sojoji ke baiwa jama'a
- An kai agaji sansanin yan IDP da magunguna
Sojin saman Najeriya sun fara aikin agaji a yankin da Boko Haram ta dai-dai-ta, inda suke bada magunguna, abinci da agaji ga kayan masarufi ga wadanda bala'in ta'addanci ya koro daga gidajensu.
Zasu share makonni biyu suna wannan atisaye a garin Maiduguri da Damboa da ma wasu sansanonnin na masu gudun hijira.
DUBA WANNAN: Biyan miliyoyi da ake yi wa Boko Haram ya sasu sace matan Dapchi
Wannan na zuwa ne shekara daya bayan da sojin suka saki bam bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijiran a Rann, inda 160 suka mutu, a zaton sojin, wai Boko Haram ne suke taro a wurin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng