Gidan sama mai hawa biyu ya rushe a jihar Legas
- Gidan sama mai hawa biyu ya rushe a jihar Legas
- Rahotanni sum nuna mutane 11 sun ji rauni
Wani gidan sama mai hawa biyu ya rushe a community road, dake unguwar old otta Alagbado a jihar Legas
Wannan al’amari ya faru ne a ranar Lahadi 25 ga watan Febarairu, 2018 da misalin karfe 4.30. na safe
A lokacin da Legit.ng ta samu wannan rahoton , an riga an kai mutane 11 a asibitin Merit dake Legas, kuma har yanzu ba a gama tatancewa ba ko akwai wanda suka mutu.
Hukumar kawo ba da agajin gaggawa (NEMA)sun isa wajen dan taimakawa. Kuma sun rufe wajen dan bincike.
KU KARANTA : Cacar baki ya barke tsakanin rundunar Soji da gwamnatin Yobe Kan 'Yan Matan Dapchi
A rahoton da kungiya kula da biranai suka fitar, sunci sama da gidaje 35 suke rushe wa kowani shekara a Najeriya.
Kuma akalla mutane 200 suke samun rauni ta wannan hanyar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Source: Hausa.legit.ng
Asali: Legit.ng