Duk qanzon kurege ne, babu wani matsin tattali da Buhari ya fitar da Najeriya - Atiku Abubakar

Duk qanzon kurege ne, babu wani matsin tattali da Buhari ya fitar da Najeriya - Atiku Abubakar

- Ana bakin talauci a kasar nan musamman bayan zabukan 2015

- Atiku Abubakar ya dora laifin kan Buhari

- Gwamnati tace lallai ta fitar da tattalin arzikin kasar nan daga matsi

Duk qanzon kurege ne, babu wani matsin tattali da Buhari ya fitar da Najeriya - Atiku Abubakar
Duk qanzon kurege ne, babu wani matsin tattali da Buhari ya fitar da Najeriya - Atiku Abubakar

A kokarin Alhaji Atiku Abubaakar na PDP na fara kamfe gabanin zabukan da za'a shiga a kasar nan, tsohon mataimakin shugaban kasar yace daga yadda ake wahala a kasar nan, ga alama ba'a fitar da tattalin arzikin nan daga kangin recession ba.

A ziyarar da ya kai Yola dai, jiharsa, bayan dumbin jama'ar da shugaba Buhari ya tara ba ko sisi a makon nan, Atiku ya watsa wa talakawa tsaba inda suka dumbuza suka yi wawa, karin alamu da ke nuna akwai matsuwa a tsakanin al'umma.

DUBA WANNAN: Biyan miliyoyi da ake yi wa Boko Haram ya sasu sace matan Dapchi

A 2019 dai, ana sa rai Atiku zai fafata ne da shugaba Buhari idan ya kayar da masu neman kujerar irinsu Alh,. Sule Lamido, Shekarau da watakil kwankwaso in ya koma jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng