Dandalin Kannywood: Mazajen aure muke nema - inji Gimbiya da Sa'adatu na Dadin Kowa
- Mazajen aure muke nema - inji Gimbiya da Sa'adatu na Dadin Kowa
- Sun ce rawar da suke takawa a cikin wasan Dadin Kowa yayi kusa da irin rayuwar su ta gaske
- Sun yi jinjina tare da godiya da dumbin masoyan su a duk inda suke a fadin duniya
Fitattun fuskokin nan na wasan kwaikwayon Dadin Kowa da ake haskawa a tashar tauraron dan adam ta Arewa 24 kuma daya daga cikin 'yan biyun masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood watau Gimbiya da kuma Sa'adatu sun bayyana cewa suna addu'ar Allah ya kawo masu mijin aure suma.
KU KARANTA: Yadda wani ya auri kanwar sa a Anambra
Su dai jaruman sun bayyana cewa kamar sauran mata, suma suna addu'a Allah ya kawo masu miji mai nagarta domin su samu su yi aure domin acewar su cikar darajar mace a dakin mijin ta. Sai dai muna burin mu yi aure tare, hakan ne ma ya kawo jinkirin auren, domin da a ce daban-daban za mu yi da tuni mun yi.
Legit.ng haka zalika ta samu dai cewa jaruman kuma sun bayyana cewa irin rawar da suke takawa a cikin wasan kwaikwayon Dadin Kowa yayi kusa da irin rayuwar su ta gaske.
Daga karshe kuma jaruman sun bayyana cewa a shirye su ke su ajiye sana'ar fim gaba daya indai har za suyi aure.
Haka nan kuma jaruman sun yi jinjina tare da godiya da dumbin masoyan su a duk inda suke a fadin duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng