Zafin kishi: Wani mutum ya kashe matar sa saboda tsananin kyawun ta

Zafin kishi: Wani mutum ya kashe matar sa saboda tsananin kyawun ta

- Wani mutum ya kashe matar sa saboda tsananin kyawun ta

- ma'auratan da suka shafe shekaru da yawa a tare suna da 'ya'ya biyar

- A baya an zargi mijin da matsalar tabin hankari amma sai aka ce ya warke

Wani labari maras dadin ji da muka samu daga majiyar mu ta Punch na nuni da cewa wani bakanike mai gyaran tayar mota a garin Mbiabam Ibiono na karamar hukumar Ibiono Ibom a jihar Akwa Ibom mai suna Nkere Uta ta make matar sa mai suna Bella Uta har lahira a jiya Litinin.

Zafin kishi: Wani mutum ya kashe matar sa saboda tsananin kyawun ta
Zafin kishi: Wani mutum ya kashe matar sa saboda tsananin kyawun ta

KU KARANTA: Yadda wani katon asara ya auri kanwar sa

Kamar dai yadda muka samu, ma'auratan da suka shafe shekaru da yawa a tare suna da 'ya'ya biyar kafin aukuwar lamarin da yayi matukar girgiza al'ummar yankin.

Legit.ng dai ta samu cewa ana zargin mijin ta ne da aikata wannan mummunar ta'asar saboda tsananin kishin da ke gareshi da kyawon da Allah ya yi mata shi kuma bai da kudi sosai.

Haka nan kuma majiyar ta mu ta samu cewa a baya an zargi mijin da matsalar tabin hankari amma sai aka ce ya warke.

Yanzu haka dai yana hannnun jami'an 'yan sanda.

A wani labarin kuma, Wani lamari mai cike da daure kai ya auku a jihar Anambara dake yankin kudu maso gabashin kasar nan inda muka samu labarin cewa wani malamin lissafi a makarantar sakandare a karamar hukumar Aguata mai suna Chiadikobi Ezeibekwe, ya auri kanwar sa ta jini.

Kamar dai yadda muka samu shine kanwar ta sa da ya aura tana da shekara 17 ne a duniya kuma Mista Chiadikobi Ezeibekwe ya bayyana cewa Allah ne ya kaddara zai auri kanwar ta sa inda ya kuma ce shi bai yi nadamar aikata hakan ba domin kuma ko a cikin addinin kiristanci ba bu inda aka haramta hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng