Farashin gangar danyen mai ya yi tashin da bai taba yi ba tun kafin hawan Buhari

Farashin gangar danyen mai ya yi tashin da bai taba yi ba tun kafin hawan Buhari

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa kawo yanzu dai farashin gangar danyen mai ta tashi ya zuwa akalla $71 a karon farko tun kafin shugaba Buhari ya anshi karagar mulki a shekarar 2014.

A shekarar ne dai da 2014 farashin danyen man yayi faduwar tsohuwar guzuma wanda hakan ne kuma ya nemi durkusar da tattalin arzikin Najeriya tare kuma da yin matukar barazana ga darajar kudaden mu.

Farashin gangar danyen mai ya yi tashin da bai taba yi ba tun kafin hawan Buhari
Farashin gangar danyen mai ya yi tashin da bai taba yi ba tun kafin hawan Buhari

KU KARANTA: Jerin sunaye 105 na 'yan matan Dapchi da aka sace

Legit.ng ta samu cewa da wannan ne dai 'yan Najeriya ke ta kara sa ran wata kila lamurra su dan kara canzawa tare da kara kyau musamman ma game da farashin kayan masarufi da kuma tattalin arzikin su.

A wani labarin kuma, Wata kungiya da ba ta gwamnati ba dake rajin tabbatar da kyakkyawan shugabanci da wakilci na garin mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) a turance ta shawarci gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari game da yadda za'a iya kawo karshen karin tabarbarewa cin hanci da rashawa.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyar ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) ta yi wannan kiran ne ga shugaba Buhari biyo bayan wani sabon jadawali da wata babbar kungiyar duniya dake sa ido akan matsalar cin hanci da rashawa ta duniya watau Transparency International (TI) ta fitar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng