Jami'an 'yan sanda sun kama daliban sakandare 5 dauke da cikin shege
- Jami'an 'yan sanda sun kama daliban sakandare 5 dauke da cikin shege
- Sun dai shaidawa manema labarai cewa wadanda aka kama din dalibai ne da ba su wuce shekaru 16 zuwa 19 ba
- Babban dalilin su na kama daliban shine domin yaki da yawaitar ciki barkatai
Jami'an tsaro na 'yan sandan kasar Tanzania dake nahiyar Afrika ta sanar da samun nasarar kama wasu mata akalla 5 daliban Sakandare a kasar dukkan su dauke da juna biyu inda a halin yanzu suke taimakawa jami'an tsaron domin gano iyayen su.
Jami'an tsaron na 'yan sanda dai sun shaidawa manema labarai cewa wadanda aka kama din dalibai ne da ba su wuce shekaru 16 zuwa 19 ba a duniya.
KU KARANTA: Mafi yawancin 'yan Boko Haram ba musulmai ba ne - Rahoto
Kamar yadda muka samu kuma, haka zalika sun bayyana cewa babban dalilin su na kama daliban shine domin yaki da yawaitar ciki barkatai.
Legit.ng dai ta samu cewa tuni wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba da kuma wasu na sa kai suka yi Allah-wadai da wannan kamun da aka yi wa matan.
A wani labarin kuma, A wani kokari na rufe dukkan wata hanya da asirin sa zai iya tonuwa na yin mu'amala da daya daga cikin mabiyan cocin sa, wani babban malamin addinin kiristanci mai suna Fasto Chidiebere Okoroafor ya kashe akalla mabiyan na sa su 3.
Faston mai shekaru akalla 32 dai asirin sa ya tonu ne bayan da jami'an 'yan sandan jihar Ribas suka samu nasarar cafke shi da hannu dumu-dumu cikin kisan hade kuma da wani jariri wanda ba'a kai ga haihuwa ba.
Haka zalika ma dai ayin da 'yan kasar Najeriya ke cigabda da jimamin babban ibtila'in da ya faru na sace wasu 'yan mata a makarantar garin Dapchi, jihar Yobe da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nan na Boko Haram suka yi a satin da ya gabata, yanzu an samu jerin jadawalin sunayen.
Legit.ng dai ta samu har ila yau cewa duk da wasu rahotanni da suka ruwaito cewar sojojin kasar sun kubutar da 'yan matan, har yanzu babu wani cikakken bayani game da sahihancin hakan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng