Zuwa na Najeriya na farko na hadu da wani Direba mai amana - Brimelowa

Zuwa na Najeriya na farko na hadu da wani Direba mai amana - Brimelowa

- Wata Baiwar Allah daga kasar waje ta yabawa halin Yan Najeriya

- Brimelowa tace ta manta da jakar ta a cikin motar haya a Abuja

- Bayan ta kira lambar wayar ta ne aka dace aka maido mata jakar

Mun samu labarin yadda wani Direban karamar mota ya jawowa Najeriya abin yabo a idon Duniya bayan da ya maidawa wata Baiwar Allah kayan ta da ta manta da su a cikin motar sa. A cikin jakar akwai takardun ta da fasfo.

Zuwa na Najeriya na farko na hadu da wani Direba mai amana - Brimelowa
Misis Birmelow ta nuna amanar ‘Yan Najeriya

Kirsty Brimelow wanda tana cikin manyan Lauyoyin kasar Birtaniya ta bayyanawa Jaridar Daily Trust yadda wani Direba a Birnin Tarayya Abuja ya maido mata jakar ta da ta bari a cikin motar sa lokacin tana cikin gaggawa.

KU KARANTA: Ministar Jonathan ta samu babban matsayi a kasar waje

Misis Brimelow ta bayyana cewa a lokacin da ta manta da ‘yar jakar ta a cikin motar wannan Bawan Allah har ta saduda don kuwa ta dauka shi ke nan ba za ta kara ganin sa ba bayan tayi ta kirar wayar ta da ta bari a motar.

Wannan mata ta kara da cewa bayan ta kira wayar ta gaji kurum sai wannan mutumi ya amsa kuma ya zo har inda ta ke ya kawo mata jakar ta. Wannan Baiwar Allah tace lokacin ne karon farko da ta fara zuwa Najeriya a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng