Mutuwa rigar kowa: Jirgin kasa ya markade wani mutum a garin Abuja

Mutuwa rigar kowa: Jirgin kasa ya markade wani mutum a garin Abuja

Labarin da muke samu daga majiyar mu dai yana nuni ne da cewa jirgin kasa dake jigilar jama'a yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi mai shekaru 27 a duniya mai suna Paul a garin Abuja bayan da ya rumurmutse shi, jiya Juma'a da safe.

Da mahaifin matashin na karin bayani ga manema labarai, Mista Francis Idoko ya bayyana cewa lamarin yayi matukar kada masa hanta domin kuwa mutuwar ta girgiza shi matuka.

Mutuwa rigar kowa: Jirgin kasa ya markade wani mutum a garin Abuja
Mutuwa rigar kowa: Jirgin kasa ya markade wani mutum a garin Abuja

KU KARANTA: Wani malamin addini ya kashe mabiyan sa 3

Legit.ng ta samu cewa mahaifin mamacin ya kara da cewa sun yi bankwana da dan na sa da safiyar juma'ar kafin ya fita zuwa wajen aiki har ma ya karbi Naira 200 a hannun sa da zai hau tasi.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja kuma daya daga cikin manyan dattawan arewa mai suna Janar Yakubu Gowon da safiyar yau ya jagorancin sauran mambobin wata kungiya dake yi wa kasa addu'a mai suna 'Nigeria Prays' a zuwa jihar Borno, garin Maiduguri.

Kamar yadda muka samu, gwamnan jihar ta Borno, Alhaji Kashim Shettima shi ne ya tarbi tsohon shugaban kasar sannan kuma yayi masa addu'ar samun nasara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng