Baranbarama: Wani babban malamin addini ya kashe mabiyan sa su 3
A wani kokari na rufe dukkan wata hanya da asirin sa zai iya tonuwa na yin mu'amala da daya daga cikin mabiyan cocin sa, wani babban malamin addinin kiristanci mai suna Fasto Chidiebere Okoroafor ya kashe akalla mabiyan na sa su 3.
Faston mai shekaru akalla 32 dai asirin sa ya tonu ne bayan da jami'an 'yan sandan jihar Ribas suka samu nasarar cafke shi da hannu dumu-dumu cikin kisan hade kuma da wani jariri wanda ba'a kai ga haihuwa ba.
KU KARANTA: Sulhu: Ina goyon bayan kwamitin Tinubu - Oyegun
Legit.ng ta samu dai cewa wadanda Faston ya kashe sun hada da Concilia Ezeawa da kuma Uluoma Onweagba wadan da aka ruwaito ya shakare har lahira a cikin wani ginin da ba'a kammala ba.
A wani labarin kuma, Jami'an tsaro na 'yan sandan kasar Tanzania dake nahiyar Afrika ta sanar da samun nasarar kama wasu mata akalla 5 daliban Sakandare a kasar dukkan su dauke da juna biyu inda a halin yanzu suke taimakawa jami'an tsaron domin gano iyayen su.
Jami'an tsaron na 'yan sanda dai sun shaidawa manema labarai cewa wadanda aka kama din dalibai ne da ba su wuce shekaru 16 zuwa 19 ba a duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng