Abun alfahari: An fara rububin doyar kasar nan a Dubai, Canada da Australia
- Tun bayan hawan Buhari a 2015 aka fara habaka harkar noma
- Anfara fitar da doya kasashen waje a bara, inda ake sayar da ita da dala
- Doyar tayo armashi, bayan da yanzu ake neman ta a wasu kasashen ruwa a jallo
Kasashen UAE watau Dubai, da Australiya da ma Canada sun fara marmarin doya daga Najeriya, inda sukan aiko a saya musu a jiragen ruwa. Wannan babban abin alfahari ne ga kokarin gwamnati na fitar da kaya kasashen waje.
A bara ne dai aka fara fitar da doyar kasashen waje irinsu Amurka da Ingila da sauran kasashen Turai da ma Yammacin duniya.
Sai dai wasu masu sharhi suna sukar abin bisa la'akari da uwar tsada da doyar ta fara saboda ajinta ya karu, da ma kuma rashin isar abinci a wurin talakka.
DUBA WANNAN: An gurfanar da Albarnawi dan ta'adda a gaban kotu
Tan 480 ne na doyar dai yanzu ake fitarwa kasashen waje maqare a jiragen ruwa, kuma a samo daloli a tunkudo cikin aljifan 'yan Najeriya, musamman manomanta da gwamnati, wanda hakan zai kara tattalin arziki da jari.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng