Zabarmawa basu son Hausawa - inji Sanusi Jaku

Zabarmawa basu son Hausawa - inji Sanusi Jaku

- Wani mai bawa shugaban kasar Nijar shawara yana neman hura wutar rikicin kabilanci a kasar

- Ya bayyana cewa kabilar Zabarmawa basu kaunar kabilar Hausawa

- Ya fadi hakan, saboda kawo masa farmaki da kabilar suka yi wanda babu gaira babu dalili

Zabarmawa basu son Hausawa - inji Sanusi Jaku
Zabarmawa basu son Hausawa - inji Sanusi Jaku

An fara sa-in-sa mai karfi a jamhuriyyar Nijar, inda dubban mutane a kasar ke faman zagi da tofa albarkacin bakin su ga mashawarcin shugaban kasar, Sanusi Jaku, wanda suke zargi da kokarin tada rikicin kabilanci a kasar.

A ranar 4 ga watan Fabrairun wannan shekarar, mai bawa shugaban kasar shawara yayi ikirarin cewa, hadakan jam'iyyun siyasa na adawa (FOI) sun ci mutuncin sa, tare da neman halaka shi babu gaira babu dalili.

DUBA WANNAN: Jinin Musulman Arakan ba abin banza bane, ya kamata a kawo karshen cin zarafin da ake yi musu

Abinda yasa ya nufi gidan rediyon amfani, inda ya ce, Zabarmawa wadda ita ce kabila ta 2 a Nijar fannin yawa, wanda suke da kaso 22 cikin 100, suna kyamar Hausawa, wanda sune kabila mafi rinjaye a kasar, inda suke da kaso 53 cikin 100.

Furucin nashi yayi matukar bakanta wa 'yan kasar rai, musamman ma Zabarmawa wadanda suka ce Jaku ya ci mutuncin kabilarsu, sannan kuma hakan kaman kokari ne na hura wutar kabilanci a kasar.

A ranar Litinin dinnan data gaba ta kafafen yada labarai na Jamhuriyyar Nijar, suka bayyana cewar, an kama Sanusi Jaku da shugaban tashar rediyo ta amfani, Grema Bukar zuwa babban ofis din hukumar 'yan sanda, daga bisani kuma aka gurfanar dasu a gaban kotu don jin mai zasu ce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng