Daga cin biskit, dalibai suka mutu a wani makarantan Abuja
An kulle wani makarantan gwamnati da ke unguwar Kubwa, babban birnin tarayya Abuja ranan Juma’a inda aka mayar da dukkan dalibai gida.
An kulle wannan makaranta ne bayan wasu daliban makarantan guda uku suka rigamu gidan gaskiya daga cin biskit a wani taro.
Har yanzu dai ana gudanar da bincike cikin wannan al’amari.
Wasu daliban makarantan mai suna Government Secondary School, Kubwa 1, Phase 4, sunce shugaban makaranta ya fada musu su koma gida ba tare da wani dalili ba.
KU KARANTA: An gurfanar da Al-Barnawi, shugaban 'Yan Ansaru, a gaban kotu a Abuja
Zaku tuna cewa kwanakin baya wasu daliban makaranta a gari Abuja sun yi mumunan hadari a motan makarantan da ke kai yara gida.
Masu sharhi sun bayyana yadda direbobin motocin makarantu ke gudun ganganci da yaran mutane a manyan titunan Abuja.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng